By Victor Okoye
Abuja, April 13, 2022 – Duba da yadda wakilci ke gudana a zuru na majalisar dokoki ta jaha wakilci na rashin kawo wanni aiki na cigaba daga wakilinmu hakan yassa mukayi kiraga masu ruwa da tsaki wajen tsaida y’an takara da suyi nazari wurin tsaida muna da d’an takara matashi wanda keda niyar ciyarda k’asarmu gaba wato Mallam Nasir Usman Sami
Domin shine matashin da muka ga zai iya tsayawa ya yiwa al’umma aikinda suka turashi yayyi dalili kuwa shine shi wannan matashi bai rik’e da wata kujera da hakk’inmu ya rataya akansa amman a hakan yake iya k’ok’arinsa na ganin ya taimakawa al’ummar k’asarmu ta zuru.
Yabada tasa gudunmuwa ta hanyar samarwa al’umma abubuwan more rayuwa kamar haka: gina rijiyoyi a wasu k’auyukan zuru, gyara bultsace na ruwansha a unguwanni da dama cikin garin zuru da k’auyukanta, tallafawa mata ta hanyar koya musu sana’a dun su zama masu dogaro dakai, kawo “solar” a wuraren dake buk’atar haske, tallafawa d’alibbai domin cigaba da karatunsu cikin sauk’i dadai sauran wasu gudunmuwa ga al’ummar garin zuru da kewayenta.
Idan zamuyi la’akari da irin wannan gudunmuwa da wannan matashi ke badawa a wannan yanki namu tun baida alhakin yin hakan agaremu ganin damarshine yin hakan toh ya muke gani zata kaya idan har yassamu zama wakilinmu?
Mallam Nasir Usman Sami ashirye yake da ya kawomuna ayukkan cigaba a k’asarmu ta zuru.
D’an kwalanga Allah ubangiji ya cikama burinka na zama wakilinmu na zuru a majalisar dokoki ta jaha.
Hrh Sarki Danga

































